An gano Wasiu Dauda da Al-Ameen Ibrahim, kananan yara yan shekaru hudu da aka sace a unguwar Ijesha da ke Legas. Daily Trust ta rahoto ...
An gano Wasiu Dauda da Al-Ameen Ibrahim, kananan yara yan shekaru hudu da aka sace a unguwar Ijesha da ke Legas.
Daily Trust ta rahoto cewa an gano yaran da ransu a cikin wata tsohuwar karamar motar bus a babban titin Oshodi-Apapa a safiyar yau.
Mahaifiyar Dauda, Awau, ta shaidawa wakilin Daily Trust cewa a halin yanzu yaran suna can likitoci na basu kulawa a asibiti.
"Mun gano su. An tsince su a cikin wata tsohuwar karamar motar bus a kan babban titi a safiyar yau. Yanzu haka suna asibiti," a cewar mahaifiyar da ke cike da murna.
An gano kananan yaran sun bata ne misalin karfe 4 na yammacin ranar Juma'a, awa biyu bayan sun dawo daga makaranta.
An ce wani mutum ne ya yi musu dabara ya basu biskit a lokacin da suke wasa ya shiga da su cikin adaidaita sahu ya tsere da su.
X
No comments