Jerin Jaruman Marigayen Kannywood Da Suka Furta Wata Magana wadanda suka ratsa zukatan mutane kwarai da gaske Anyi Mutuwa Data Taba Jam...
Jerin Jaruman Marigayen Kannywood Da Suka Furta Wata Magana wadanda suka ratsa zukatan mutane kwarai da gaske
Anyi Mutuwa Data Taba Jamaa Sosai Da Sosai A Kannywood Sai Da Wannan Jaruman Suna Daya Daga Cikin Mutuwa Da Ta Girgiza Nasanaantar Kannywood Inda Zamu Kawo Muku Dalla Dalla
1. Hajiya Zainab Musa Booth Tsohuwar jarumar Kannywood ce wadda ta yi kaurin suna Sosai Da Sosai a matsayin Uwa a masana'antar, galibin fina-finanta ta fito ne tare da diyarta Maryam wadda kuma fitacciyar jaruma ce.
Zainab Booth ta rasu ne a sakamakon wani ciwon kwakwalwa da ta yi mata, kamar yadda diyarta Maryam ta bayyana hakan a shafinta na Instagram.
Sai dai kafin rasuwarta, Zainab Booth tsohuwar jarumar ta kasance mai yawan karatun kur’ani mai tsarki wadda masoyanta suka burge ta sosai duk da cewa tana cikin mawuyacin hali amma ba ta yi kasa a gwiwa ba.
2. Sani Garba SK fitaccen jarumin da ya dade a masana’antar Kannywood. Baya ga jarumi Sani yana daga cikin wadanda suke yabon Annabi Muhammad S.A.W tun kafin ya shiga masana'antar Kannywood.
Sani garba Sk yayi fama da matsananciyar ciwon suga wanda hakan ya sa jarumin ya daina ayyukansa tare da neman taimako daga wajen Abokan Aiki da mutane saboda Tsananin ciwon ya kara tsananta.
Bayan 'yan makonni an kai shi asibiti don yi masa magani Da Wani Dan Siyasa Ya dau Nauyi amma daga bisani yanayinsa ya sake yin tsanani kuma ya rasu a ranar 15 ga Disamba 2021. Allah Ya Jikan Rai
Amma kafin rasuwarsa, an sha ganin jarumin a wasu wuraren da suka saba haduwa domin yabon Manzon Allah SAW duk da cewa yana Fama Da ciwo Kuma Yana cikin mawuyacin hali, amma duk lokacin da aka gayyace shi yakan kai ziyara. Allah Ya Jikan Sa Ammen
3. Rabilu Musa Ibro wanda aka fi sani da ibro Wasu Kuma Na kiranka Da Chairman ana kiransa da sarkin wasan barkwanci na Hausa, Ibro dai ya shahara sosai kuma yana daya daga cikin fitattun jaruman barkwanci a masana'antar Kannywood, Ciki Da Waje Rabilu Musa ibro ya rasu a shekarar 2014 sakamakon ciwon koda. A Asibiti
A wata hira da Akayi Da Falalu wani dorayi wanda fitaccen jarumi ne kuma darakta a masana’antar, Falalu ya bayyana cewa da wuya a samu wanda zai maye gurbinsa. Gaskiya Dai A Wannan Lokaci
Daya daga cikin ‘ya’yan marigayin na biyar ya ce a lokacin da mahaifinsu ya kusa rasuwa ya tara su wuri guda ya shawarce su da cewa duk abin da za su yi a rayuwa su kasance masu gaskiya da gaskiya
.
No comments