Muna Yin Fim Ne Domin Gyaran Tarbiyya, Cewar Ruƙayya Umar (Dawayya) Daga MUKHTAR YAKUBU Fitacciyar jaruma a Masana'antar Kannywwod, R...
Muna Yin Fim Ne Domin Gyaran Tarbiyya, Cewar Ruƙayya Umar (Dawayya)
Daga MUKHTAR YAKUBU
Fitacciyar jaruma a Masana'antar Kannywwod, Rukayya Umar Santa, wadda aka fi sani da Rukayya Dawayya. Ta yi Kira ga Jama'a da su rinka yi musu kallon mutane da su ke yin sana'ar su kamar yadda sauran Jama'a su ke gudanar da harkar kasuwancin su da sana'o'in su.
Jarumar ta bayyana Hakan ne a lokacin da muke tattaunawa da ita a game da irin kallon da a ke yi wa Yan fim musamman Mata.
Rukayya Dawayya ta ce "Ina son mutane su kalle mu a matsayin ya'yan wadansu da aka yi aure aka same su.
Kuma iyayen mu suka ba mu tarbiyya suka saka mu a makaranta muka samu ilimi, don haka duk abin da muke yi ba don mu bata tarbiyyar wani ba ne, Kuma ni na dauki harkar fim a matsayin sana'a, kamar yadda kowacce Mace mai aiki da take tafiya aiki. To haka mu ma muke da fim din mu.
Saboda haka duk wajen da aka gammu aiki mu ke yi kamar sauran mata masu aiki, don haka mu Kan sa a ran mu mun tafi neman hakalne, don haka sai a rinka yi mana addu'a a rinka yi mana kallo na adalci, domin mu ma muna da hakkin mu yi rayuwa kamar kowa a matsayin mu na Yan kasa. "
Daga karshe ta yi fatan masu harkar fim za su hada Kan su domin ciyar da Masana'antar Kannywwod gaba.
