Ni Kaina Ina Mamakin Yadda Na Zama Riƙaƙƙen Dan Bindiga, Cewar Bello Turji Kasurgumin dan bindigar nan na Jihar Zamfara, Bello Turji, wanda...
Ni Kaina Ina Mamakin Yadda Na Zama Riƙaƙƙen Dan Bindiga, Cewar Bello Turji
Kasurgumin dan bindigar nan na Jihar Zamfara, Bello Turji, wanda ya shahara wajen garkuwa da mutane ya bayyana cewa shi kansa yana mamakin kasancewarsa dan bindiga.
Bello Turji, wanda ake zargi da yawancin ta’asar da ake aikatawa a yankin Arewa maso Yammacin kasar, ya bayyana hakan ne a cikin hirarsa da shahararren ma’aikacin jaridar Daily Trust, Abdulaziz Abdulaziz.
A cewarsa, da a shekarun baya idan aka ce zai zama shahararren dan bindiga ba zai taba yarda ba.
Ya ce a lokutan baya yana zuwa wurin sarkin Shinkafi kuma shima sarkin Shinkafi ya san shi, kuma yana zuwa har gurinsa.
A wancan lokacin inda za a ce zan zama rikakken dan bindiga, saboda kowa yasan mu Fulani ba barayin shanu ba ne, amma yadda ake mana ne ya sa muma dole mu ka sauya.
Ya kara da cewa, ayyukan ‘yan sa kai na daga cikin abubuwan da suka kara ta’azzara wannan rikici na ’yan bindiga tare da tursasa shi da sauran matasa zama ’yan ta’adda.
No comments