Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

Yanzu Yanzu Aliyu Sani Madaki Yayi Wa Shugabancin Buhari Da Shi Buharin Kansa Kaca Kaca Abubuwan Dake Faruwa A Kasar

Yanzu Yanzu Aliyu Sani Madaki Yayi Wa Shugabancin Buhari Da Shi Buharin Kansa Kaca Kaca Abubuwan Dake Faruwa A Kasar  #BUHARIMUSTGO Shug...


Yanzu Yanzu Aliyu Sani Madaki Yayi Wa Shugabancin Buhari Da Shi Buharin Kansa Kaca Kaca Abubuwan Dake Faruwa A Kasar

 #BUHARIMUSTGO

Shugaban kasa Muhammadu Buhari magana ta gaskiya bashi da imani kuma 

bashi da tausayi.Iftila’in da ya samu jama’a ranar litinin da daddare cikin jirgin kasa kusa da shiga kaduna ya tabbatar rashin tausayin sa da imani.Jama’a su tuna cewa bandits/terrorists sun bada notice tun sanda suka fara tare jirgin kasa on same route amma ba’a dauki wani mataki ba saboda zalinci.

Abun mamaki wai jiya bayan wannan masifa,Shugaba bai iya zuwa wajen don gani da idonsa ko yaje kaduna duba mutane ba.Malamai da suke kuka suna cewa da ayi zalunci suna kallo basuyi magana ba gara sun mutu,amma kaji su tsit.

Mutanan Nigeria Musanman mutanan Arewa dole mu futo mu kwaci yancin kanmu ko kuma,duk mu wulakanta a hannun mugun Shugaba da ya rantse da Alqu’ani zai kare rai da lafiyar al’umma amma yaki yi.

Jama’a mu futo mu kwaci kanmu ko azzalimin shugaba ya tozarta mu.Mu futo muyi zanga zanga saiya sauka domin bai iyaba kuma bazai iyaba.

Aliyu Sani Madaki

Tsakanin mu da azzalumun shugaba sai Allah Ya isa.

Ads h