A Umarar Ban Jaruma Nafisa Abdullahi Ce Kadai Ta Samu Zuwa Aikin Umara Na Bana A Yan Matan Kannywood A Umarar Bana Mun Hango Jarumar F...
A Umarar Ban Jaruma Nafisa Abdullahi Ce Kadai Ta Samu Zuwa Aikin Umara Na Bana A Yan Matan Kannywood
A Umarar Bana Mun Hango Jarumar Fina Finan Hausa Wadda Aka Fisani Da Nafisa Abdullahi Mun Hango Ta Ita Daya Tilo A Masanaantar Kannywood Din Ita kadaice Ta Samu Ziyartar Dakin Allah A Wannan Karon
*A CIKIN MATAN KANNYWOOD NAFISA CE KADAI TAJE UMRAH*
*"Yabon Gwani ya zama dole"* inji Hausawa. Wannan karin maganar ya dace da labarin da muke shirin wallafa muku akan jaruman *Kannywood.*
Kamar dai yadda kuka sani Kannywood masana'antar fim ce wadda ta shahara saboda girman ta da kuma tarin hazikan jarumai daga ko'ina a sassan Nijeriya kai harda ma wasu kasashen ketare. Hakan ne yasa masana'antar ta zama masana'antar fim mafi girma da take yada shirye shiryen ta da babban yaren kasa domin aika sakonnin kai tsaye.
A duk shekara akan sami rige rige da gasa a tsakanin matan kannywood wajen zuwa dakakin *Ka'abah* dake kasar *Saudiyya* domin gudanar da aikin *Umrah,* to amma abin mamaki a wannan shekarar abin ba haka yake ba domin kuwa an sami jaruma daya tilo da ita kadai ce ta ziyarci Dakin Allãh domin gudanar da aikin Umrah cikin watan *Azumi.* Jarumar kuwa ba wata bace face shahararriyar jarumar nan mai suna *Nafisa Abdullahi* hazika kuma kyakykyawar jaruma son kowa.
Sauran jaruman kuma sun dauki saiti izuwa wasu kasashen irin su Dubai da sauran su, domin yawon bude ido. Domin kuwa an hango wasu matan Kannywood kai harda maza ma suna ta cin duniyar tsinke. Wani ma harda matar sa sabon aure.
*Hajiya Nafisa Muna fatan Allãh Ya karbi aikin Umrahr ki da na ilahirin 'yan'uwa Musulmi. Allãh Ya karbi ibadun mu baki daya.
*YAKUBU ADAM ABUBAKAR (YACKSON)*
No comments