Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

Sabuwar Wakar NNPP Tare Da Aminu Bagwai Da Mai Barkwanci Nakowa A Wakar Sulaimam Hunkuyi Kaduna

  Sabuwar Wakar NNPP Tare Da Aminu Bagwai Da Mai  Barkwanci Nakowa A Wakar Sulaimam Hunkuyi  Kaduna Wannan Waka Ta Aminu Da Mai Barkwanci ...

 

Sabuwar Wakar NNPP Tare Da Aminu Bagwai Da Mai

 Barkwanci Nakowa A Wakar Sulaimam Hunkuyi Kaduna

Wannan Waka Ta Aminu Da Mai Barkwanci Wato Nakowa Ta Samu Aiki Mai Kyaw inda Akayi Mata Aiki Mai Kyu sosai Da Sosai Aminu Bagwai Ada Dai Munga Yana jamiyar A.P.C Amma Yanzu Munga Ya Koma NNPP Ind mukaga Ya Bulla Ta Gidan Hukuyi Kaduna Inda


*SABUWAR WAKAR NNPP TARE DA AMINU BAGWAI*

Shararren mawakin siyasar nan Aminu Bagwai ya tashi kan kowa inda ya saki wata sabuwar waka wadda yayiwa sabuwar jam'iyyar NNPP inda aka ganshi ya fito tare da sanannen dan wasan barkwancin nan Ale Baba Nakowa.

Wannan sabuwar wakar dai ta sami aiki mai kyau sosai ta yadda duk wanda ya saurara ko ya kalla zai so ya kara jinta ko ya sake kallon ta.

Shidai wannan mawaki ba boyayye bane domin yayi wakoki masu tarin yawa kama daga na soyayya, wakokin biki, wakokin jaje da kuma wakokin siyasa.

Tun a baya dai mawakin ya shahara kan wakokin siyasa amma a jam'iyyar APC inda daga bisani muka ji shi kwatsam a jam'iyyar NNPP kuma har ya gwangwaje su da wata waka wadda yazo mata da sabon salon da idan mai sauraro yaji ko kuma masu kallo suka kalla to ko shakka babu sai sun kara jinjina was wannan gawurtaccen mawakin domin kuwa ya zo da cikakken salo na bajinta inda yayi amfani da wasu kalamai ba duka  kai ba.

Aminu Bagwai ya kasance mawaki irinsa daya tilo da yake gabatar da nau'in da launin wakar sa mai salon yabon gwani ya zama dole domin ko tambayar ka aka yi amsar da zaka bayar itace salon Aminu Bagwai ya sha bamban da na sauran takwarorin sa mawaka. Ta wannan dalilin ne na yasa mawakin ya shahar sannan kuma ya tara dubbanin masoya a sabgar sa ta waka.

Mawaki Aminu Bagwai ya faro ta Kaduna ne inda muka ji shi ya bulla gidan Hunkuyi Kaduna inda ya wake Hunkuyi da sabuwar jam'iyyar da ya koma ta NNPP wadda ake raderadin dama can madugun kwankwasiyya Dr Rabiu Musa Kwankwaso ne ya kafa jam'iyyar. To Aminu Bagwai Allah Ya bada sa'a.

                          

 *YAKUBU ADAM ABUBAKAR (UNCLE YACKS)*

No comments