Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

Kashe Wannan Dalibar Da Aka Yi Ta'adanci Ne, Ba Aikin Annabi Bane ~ Wani Matashi

 Kashe Wannan Dalibar Da Aka Yi Ta'adanci Ne, Ba Aikin Annabi Bane ~ Wani Matashi Shifa Addinin Musulunci ba addinin kara zube bane, y...

 Kashe Wannan Dalibar Da Aka Yi Ta'adanci Ne, Ba Aikin Annabi Bane ~ Wani Matashi

Shifa Addinin Musulunci ba addinin kara zube bane, yana da dokoki da ƙa'idoji. Duk kyan aikin da kai acikin Addinin indai bakabi ƙa'idar da mai addinin ya tsara maka ba, to aikin banza kai.

Ɗaukar doka a hannu, abisa kowanne irin laifi bazai taɓa zama hanyar samar da zaman lafiya tsakanin Al'umma ba, shi kuma Musulunci gaba ɗayan sa Addinin zaman lafiya ne bana ta'addanci ba.

Zaka iya ganin kamar maganata tai tsauri, amma kome zakace gaskiya ce. Abinda akai a Sakkwato ba koyarwar Annabin da ake gani anyi domin sa bane, shima bazai maraba da É—aukar doka a hannu ba.

No comments