Nayi Zinah Da lta Sau Uku Amma Ban Yarda Cikin Dake Jikinta Nawa Bane/Ya So Yayi Lalata Da "Yarsa Wani Magidanci ne mai diya ma...
Nayi Zinah Da lta Sau Uku Amma Ban Yarda Cikin Dake Jikinta Nawa Bane/Ya So Yayi Lalata Da "Yarsa
Wani Magidanci ne mai diya mace mai shekaru 15 da haihuwa yayiwa abokinsa kofar rago bayan ya nemi yin lalata da yar abokin nasa, Shi dai magidanci yace ba ma aboki kawai ya daukeshi ba, Ya maida shi tamkar dan uwana jini, Hakan yasa yake shiga gidansa ba tare da yavi sallama ba. Abunda ya bamu mamaki muna zaune da uwar yarinyar nan sai ta samemu take nuna mana ga sakon da Uncle ya tura mata, saboda haka suke kiransa. Muna dubawa muka cika da mamaki, Nan take na cewamatata sam bazai yi haka ba, Kila dai kuskure aka samu, Na nuna abar maganar sai idan ya sake yi" inji shi.
Ya ci gaba da cewa. Suna zaune bayan kwana biyu sai ga ta kuma ta zo da wayar nata a guje ya ÅŸanmemu tace mu saurari abunda yake fadamata, Inda ta saka muryarsa a sarari muna jin abubuwan da vake fadamata na rashin daraja da mutunci.
Bayan da muka tabbatar muka gamsu shine, muka shirya masa gadan zare na zamu je unguwani da madam da sauran yaran ammaita zamu barta a gida. Bayan ya bar gidan namu ne sai ya bugo mata waya akan zai zo ya sameta idan munje unguwa. To da haka muka kamashi, lyayen yarinyar sukace ba karamin kunya suka ji ba ganin wanda ya dace ya kula da yaransu idan basu da rai shine ke kokarin lalata su. Wannan yasa mijin yaja hankalin maza magidanta masu ya'ya mata irinsa da suka kula bama da abokansu ba harma da kannensu akan hakan, Shi dai abokin sun masa jina jina suka dauke shi suka kai shi asibi. Babu abunda baya faruwa a gidajen mutane, Sai dai ba duk abubuwan da suke faruwa bane ake bari aji,
Wani magidancin da aka turo kanwar matarsa ta zo ta kula da matarsa tashi bayan ta haihu, ya sake lallabawa ya dirkawa kanwar matar tashi itama ciki. Ita dai kanwar matar tasa tace tunda tazo gidansu yake ta kerkeranta. "Da daki daya nake kwana da yayata, sai yace na koma dakin baki ina kwana shi zai rika kwana da ita, saboda ya samu damar rika zuwa mini". injita. Su dai iyayen matar dana mijin wadanda suka kayi kokarin boye maganar amma wani mai tsaigumi ya tsaigunta mini lamarin. Sun baiwa matar tasa hakuri na ta daure ta zauna gidan nasa ganin dai kanwarta ce abun yafaru da ita, Inda kuma ta basu sharadin saldai a zubar da cikin.
No comments