A nawa fahimtar akan kwankwaso za'a farayin siyasar tazarce__"Inji Matashi "Wani matashi mai suna Haidar Addis Ababa, y...
A nawa fahimtar akan kwankwaso za'a farayin siyasar tazarce__"Inji Matashi
"Wani matashi mai suna Haidar Addis Ababa, ya bayyanawa Alfijir Hausa a domin jaridar ta wallafa wannan bayanin nasa kan cewa, matukar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya samu daman mulkan Nijeriya, toh" ba shakka talakawa zasu so yayi tazarce, saboda yadda zai gudanar da mulkinsa cikin rikon gaskiya da amana."
SIYASAR KANO: Murtala Garo na shirye-shiryen ficewa daga APC
Sabuwar taÆ™addama ta kunno kai inda dan takarar kujerar mataimakin gwamnan Kano Murtala Sule Garo, wanda gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje, ke goyon baya na shirin ficewa daga jam’iyyar APC.
A cikin daren ranar Laraba Gwamna Ganduje ya isa gidan Murtala Garo domin lallashin shi ya janye yunkurinsa na ficewa daga jam’iyyar APC.
Majiyarmu ta ce ko bayan ganawar, Murtala bai nuna hakikanin matsayinsa game da zama ko ficewarsa daga APC ba, bai bayar da wata gamsasshiyar amsa ba.
You Can Read Also: Sabuwar Wakar Aminu Bagwai Ta NNPP
You Can Read Also: Aminu Bagwai Da Jarumin Barkwanci Nakowa Comedy
You Can Read Also:Sabuwar Wakar Tijjani Gandu NNPP
“Zai gana da makusantansa ya dauki matsaya, amma bai ji dadin abin da ke faruwa ba, amma bai fice daga jam’iyyar APC ba ko takararsa,” in ji majiyarmu.
Ganduje ya zabo Murtala, tsohon Kwamishinan Kananan Hukumomin ya zaman dan takarar kujerar mataimaki gwamnan jihar ga mataimakin gwamnan jihar mai ci, Nasir Gawuna, a zaben 2023 da ke tafe.
Ana ganin Murtala na barazanar ficewa daga APC ne bayan zaman sulhu da aka yi, wanda Ganduje ya hakura da neman kujerar dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kano ta Arewa, ya bar wa Sanata Barau Jibrin, wanda ba sa ga macici da Murtala.
Idan ba a manta ba, Ganduje ya hakura da neman kujerar Sanata ne bayan Barau ya jingine aniyarsa ta neman takarar kujerar Gwamnan Jihar Kano.
Majiyoyi sun ce Murtala Garo na ganin Barau a matsayin babban dan adawarsa kuma daya daga cikin shugabannin bangaren APC na G-7 da suka nemi karbe akalar jam’iyyar a jihar.
Saboda haka yake ganin bai kamata Ganduje ya karbi sanata Barau ba bayan hukuncin Kotun Koli da ya damka shugabancin jam’iyyar a hannun bangaren gwamnan.
X
Ana ganin Murtala ya damu da dadin yadda ake yawan ficewa daga jam’iyyar ta APC mai mulkin jihar ta Kano, lamarin da ke barazana ga takararsa ta 2023.
Wasu na ganin zai iya komawa jam’iyyar NNPP da ake rububin shiga a jihar, kamar yadda a baya-bayan nan tsohon gwamnan jihar, Sanata Ibrahim Shekarau ya koma.
- Aminiya
Ko me muka ce ?
