ATIKU PRODUCTION SUPPORT 2019 CAMPAIGN SONG Muna Neman Atiku Abubakar Turakin Adamawa Munyi Ne Don Kishin Damuke Gareshi 08036449143 ATIKU...
ATIKU PRODUCTION SUPPORT 2019 CAMPAIGN SONG
Muna Neman Atiku Abubakar Turakin Adamawa Munyi Ne Don Kishin Damuke Gareshi
08036449143
ATIKU ABUBAKAR WAZIRIN ADAMAWA
Wanene Atiku Abubakar?
Alh Atiku Abubakar GCON kuma Wazirin Adamawa an haife shine ranar 25 ga watan Nuwamba 1946 (25th November, 1946 a JADA wani kauye ne a yankin Kamaru da Ingla ta raina (British Cameroon) wanda daga baya aka maida kauyen cikin Tarayyar Nijeriya bayan anyi kuriar raba gardama. Sunan Mahaifin sa Garba Abubakar Fulani ne Makiyayi, Manomi kuma dan kasuwa. Sunan Mahaifiyar sa Aisha Kande, an mayar masa da Sunan kakan sa na wajen uba Daya yayi hijira daga Wurno Jihar Sokoto inda ya dawo wani kauye mai suna Kojoli a garin Jada, haka zalika Kakan sa na waje uwa da mai suna Inuwa Dutse, wanda ya yayi hijira daga Jigawa ya koma Jada.
Atiku Abubakar ya kasance da daya tilo a wajen mahaifin sa wanda tun yana karami mahaifin nasa ya rasu a yayin ketare wani rafi a kokarin sa na zuwa wani kauyen Toungo makotan Jada, anan ne Allãh Ya kar6i ransa. Allãh Ya Gafarta Masa.
KARATU
Mahaifin Atiku Abubakar ya kasance mai kyamar karatun zamani (western education) a lokacin ne ya hana Atiku zuwa Makarantair Boko yace Islamiyya kawai zai yi, daga nan ne aka kama shi aka kulle sai daga bisani Kakar Atiku Abubakar tayi belinsa. Yana dan shekara takwas ne ya gama firamare ta garin Jada a 1960 sai ya wuce Sakandaren Jada a wannan shekara inda yayi karatu tare da dalibai 59. Ya gama Sakandaren ne a shekarar 1965 ya kuma sami cinye darasi Uku a sakamakon Jarrabawar Afirka ta Yamma (WEAC). Bayan ya gama sakandare ne ya tafi makarantar horon 'Yansanda ya inda ya sami horo na dan karamin lokaci inda daga baya ya tafi Makarantar Ilimin Kiwon lafiya dake (School Of Hygiene) Kano a 1966 inda ya rike Shugaban Dalibai na Rikon Kwarya.
A 1967 Atiku Abubakar ya sami damar tafiya Jami'ar Ahmadu Bello Dake Zaria inda yayi Diploma akan Ilimin Gudanar Da Mulkin. Bayan ya kammala ne a 1969 lokacin yakin Basasa aka dauke shi aiki a Hukumar shige da fice ta Kasa (Nigeria Customs Service).
ATIKU YAYI AURE KUWA?
Atiku Abubakar GCON a halin yanzu yana da mata hudu (4 wives) da 'Ya'ya Ashirin da takwas. Atiku yace yana so ya fadada ahalin Abubakar shine ma yasa ya auri mata hudu domin baya son 'ya'yan sa suka kasance cikin kadaici kamar dai shi lokacin yana yaro shi kadai ne a wajen baban sa.[2:50 pm, 02/10/2021] YAKSON: Ya shafe shekaru ashirin yana a Huumar Kwastam inda ya zamo Mataimaki Darakta na Hukumar, daga nan ne yayi ritaya a watan Afrilu 1989. Daga nan ne ya shiga kasuwanci da siyasa gadan gadan. A 1974 ne ya ya kar6o rancen kudi Naira 31,000 inda ya gina gidan sa na farko a Yola ya kuma zuba 'yan haya.
Wani Baturen Italiya ya gayyaci Atiku Abubakar da suyi aiki tare a Kamfanin safar Kontinoni na Nijeriya watou "Nigeria Container Services (NICOTES)" da yayi aiki dasu a ga6ar tekun Legas wanda a nan ne a Atiku Abubakar ya sami kudi masu yawa, sannan kuma da da harkar Mai inda ya zama Biloniya.
Bayan Atiku ya shiga harkar siyasa lokacin Bamanga Tukur Yana Shugabancin safar Ga6ar Teku, Atiku ya zama shugaban yakin neman za6e na Bamanga Tukur a Jihar Adamawa inda kafin nan ne ya hadu da Janar Shehu Musa 'Yar'adua wanda shine ya tsunduma shi a harkar siyasa.
Shehu Musa Yar'adua ya kira taron siyasa domin kafa wata sabuwar Jam'iyya me suna PFN inda a wajen taron ne Atiku ya hadu da jigajigan 'yan siyasa kamar su: Umaru Musa, Sabo Bakin Zuwo, Bola Tinubu, Rabiu Kwankwaso, Baba Gana Kingibe, Abdullahi Aliyu Sumaila da Abubakar Koko.
A 1989 aka za6i Atiku Abubakar ya zama shugaban jam'iyyar PFN a Jamhuriya ta uku.
Atiku Abubakar ya zama Dan Majalisa mai wakiltar maza6ar sa a Adamawa a Jam'iyyar PFN a1989.
A Disamba 1990 a Atiku Abubakar ya bayyan kudirin sa na Neman gomna a Jihar Gongola wanda ba'a dade ba aka raba Jihar gida biyu, Adamawa da Taraba inda ya kasance a Jihar Adamawa ina ya ci za6en share fagen takarar Gwamna a Jam'iyya SDP wanda daga baya aka soke takarar sa.
A shekarar 1993 Atiku Abubakar ya shiga zaben share fage na Shugabancin Nijeriya, inda sakamakon ya kasance MKO Abiola ya sami kuri'a 3, 617, Baba Gana Kingibe 3,255, Atiku Abubakar 2,066. Abiola Ne ya lashe za6e ya kuma yiwa Atiku alkawarin zai dauke shi a matsayin mataimaki wanda daga baya aka rilasta Abiola ya dauki Baba Gana Kingibe.
[2:54 pm, 02/10/2021] YAKSON: A 1999 Atiku Abubakar ya zama Gwamna a Jihar Adamawa inda bayan anyi za6en shgaban kasa ne Obasanjo ya za6e shi a matsayin mataimakin sa na Shugaban Kasa a jam'iyyar PDP.
Its a Good An Stating Place For Atiku In The Year 2015 That The presidencial Election Is To Hold On Between Atiku Abubakar And Presudent Muhammadu Buhari At that Time Uts About A.p.c And P.d.p this Is why Youth in the north Thinks That The Man To Vote Is Atiku Abubakar Which is zin P.d.p the Put And Effect To see The Everthing Is Going On Smooth
This Is The Campaign Son Of Atiku Abubakar If P.d.P
YAKUBU ADAM ABUBAKAR (UNCLE YACKS)📖🖋️🖊️
We hope Atiku Will win In This Com