Page Nav

HIDE

Grid

GRID_STYLE

Tinubu ya nemi majalisa ta amince ya tabbatar da Janar Oluyede babban hafsan sojin ƙasa

 Tinubu ya nemi majalisa ta amince ya tabbatar da Janar Oluyede babban hafsan sojin ƙasa Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya aike wa majalisar...

 Tinubu ya nemi majalisa ta amince ya tabbatar da Janar Oluyede babban hafsan sojin ƙasa





Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya aike wa majalisar dattawan ƙasar buƙatar neman amincewarta don tabbatar da naɗin Laftanar Janar Olufemi Olatubosun Oluyede a matsayin cikakken babban hafsan soji ƙasa na Najeriya.


Cikin wata sanarwa da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga ya fitar ranar Juma'a ya ce Shugaba Tinubu ya aike da wasiƙar ne kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar da na dokar aikin sojin ƙasar suka tanada.


A ranar 30 ga watan Oktoba ne Shugaba Tinubu ya naɗa Janar Oluyede a matsayin muƙaddashin babban hafsan sojin ƙasan, bayan rashin lafiyar Latfanar Janar Taoreed Lagbaja, wanda ya mutu ranar 5 ga watan Nuwamban da muke ciki.


Sanarwar ta ce shugaban ƙasar na da ƙwarin gwiwa kan jagoranci da ƙwarewar Laftanar Janar Oluyede, don haka ne yake son majalisar ta tabbatar da shi, don ya jagoranci rundunar sojin ƙasa ta Najeriya domin tabbatar da zaman lafiya da tsaron ƙasar.






No comments